Rahama Sadau Ta Yi Ma Shugabannin Najeriya Allah Ya Isa Game Da Matsalar Rashin Tsaro Da Yankin Arewa Yake Ciki
Shahararriyar jarumar Fina-finan Kannywood “Rahama Sadau ta yi Allah wadai bayan harin ta’addancin da wasu ƴan bindiga suka kai a tashar jirgin ƙasa tsakanin Katari zuwa Rijana akan hanyar Abuja.shafin daily news hausa na ruwaito
Idan zaku iya tunawa a daren ranar Litinin ne wasu ƴan bindiga suka dasa abin fashewa Bom a wani jirgin ƙasa mai ɗauke da fasinjoji sama da 970 wanda ya tasa daga Abuja zuwa Kaduna inda suka kashe mutun 8 da yin garkuwa da mutun 30 tare da raunata mutane da dama daga cikin jirgin bayan sun yi nasarar tsaida shi.
Jarumar Rahama Sadau tace Najeriya kasa ce wacce ta gaza kuma shuwagabannin ta suka gaza kare rayukan al’umma.
Hakazalika Rahama Sadau ta kira shugabannin Najeriya da wadanda suka gaza tabuwa komai ga yan kasar.
Jarumar ta dora wannan bayani ne a shafinta na Twitter a cikin harshen turanci inda ta magantu akan cewa Najeriya na fama da ƙalubalen rashin tsaro.
A ƙarshe dai jaruma Rahama Sadau ta yi Allah ya isa har sau uku ga mahukuntar Najeriya.