Labarai

Pakistan: Mutane 30 sun rasu, 60 sun jikkata bayan da ɗan ƙunar baƙin-wake ya tada bam a masallaci

Wasu ƴan ƙunar baƙin-wake sun tada bam a jikinsu a wani masallaci da ke Arewa-Maso-Yammacin Pakistan, inda mutane 30 su ka rasu nan take, wajen 60 kuma su ka ji raunuka, kamar yadda ƴan sanda da likitoci su ka baiyana.Pakistan: Mutane 30 sun rasu, 60 sun jikkata bayan da ɗan ƙunar baƙin-wake ya tada bam a masallaci
Daily Nigerian hausa ta ruwaito cewa Wani jami’in ƴan sanda, Haroon Raheed ya ce ƴan ta’addan sun kutsa kai cikin harabar masallacin da ke Peshawar, bayan da su ka bindige ƴan sandan da ke garin masallacin, kafin da ga bisani su tashi ban ɗin da ke jikin su.
Tuni dai a ka garzaya da gawawwakin da waɗanda su ka ji rauni zuwa asibitin Lady Reading, wanda shi ne babban asibiti a garin.
Hukumomin na hasashen yawan mamatan zai ƙaru bayan da dama da ga cikin waɗanda su ka ji raunuka su na cikin halin rai-kokai mutu-kokai.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. Allah ya musa rahama ya tona asirin maqiya addininsa, Allah ya bawa masu raununka lafiya ya tashi kafadunsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button