LabaraiUncategorized

NNPP ta yi babban taro na ƙasa, inda ta zaɓi Farfesa Alkali a matsayin shugaban jami’ya na ƙasa

Advertisment



Jam’iyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, mai alamar kayan marmari, ta yi babban taron ta na ƙasa a jiya Laraba a Abuja, inda ta zaɓi Farfesa Rufai Alkali a matsayin shugaban jami’yar na ƙasa.daily Nigeria ta ruwaito

Jam’iyar ta zaɓi shugabannin na ta guda 30 gaba ɗayansu ta hanyar maslaha.

Wasu daga cikin shugabannin sun haɗa da Shugaban Jam’iyar na Ƙasa, Rufai Alkali daga Jihar Gombe; Mataimakin Shugaban Jam’iya na Ƙasa , AVM John Ifemeje mai ritaya (Anambra); Sakataren Jam’iya, Dipo Olayoku (Ogun) da kuma Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa, Suleiman Hunkuyi (Kaduna).



Sauran sun haɗa da Mataimakin Sakataren Jam’iya na Ƙasa, Ahmed Ajuji, (Adamawa); Ma’ajin Jam’iya na Ƙasa; Sanin Malam (Bauchi); Lauyan Jam’iya , Bem Angwe (Benue), da dai sauransu.

Da ya ke jawabi bayan ya zama Shugaban Jam’iyar, Alkali ya ce kafa jam’iyar wani tushe ne na samar da sabuwar Nijeriya.

A cewar sa, NNPP za ta yi iya kokarinta ta tabbatar da ci gaban Nijeriya da ga ko wanne ɓangare.

“Ƴan Nijeriya sun gaji kuma yanzu mafita su ke nema. To mu ne mafita kuma za mu yi iya bakin ƙoƙarin mu mu ga cewa an tafi da kowa,” in ji shi

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button