Labarai

Nijeriya ce ta 118 a jerin ƙasashe masu farin-ciki a duniya — Rahoto

Nijeriya ce a matsayi na 118 a rahoton ƙasashe masu farin ciki na 2022.
A rahoton, wanda a ke fitar da shi shekara-shekara ya nuna cewa Nijeriya na kasan ƙasashe 17 na Afirka da su ka haɗa da Afirka Ta Kudu (91), Gambia (93) Algeria (96), Liberia (97), Congo (99), Morocco (100), Mozambique (101), and Cameroon (102).
Daily Nigerian hausa ta ruwaito sauran sun haɗa da Senegal (103), Niger (104), Gabon (106), Guinea (109), Ghana (111), Burkina Faso (113), Benin (115), Comoros (116), sai kuma Uganda (117).
Sai dai kuma rahoton ya ce Nijeriya ta na saman Kenya (119), Tunisia (120), Mali (123), Namibia (124), Madagascar (128), Egypt (129), da Chad (130) a jerin ƙasashen.
Hakazalika rahoton ya ce ƙasar Finland ita ce ƙasa mafi farin-ciki a duniya, inda ta ɗare matsayin karo na biyar kenan a jere.
It kuwa Afghanistan ita ce ƙasa mafi ƙunci a duniya sai Lebanon ke take mata baya, kamar yadda rahoton ya baiyana.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button