Kannywood

Naziru sarkin waka ya cire mun kebura 99 a jikina – Fati Slow

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow Motion ta magantu a kan yadda aka karshen takkadama da ya faru a masana’antar ta shirya fina-finan Hausa kwanakin baya a hirarta da BBC Hausa.
Legit ta tattauro bayyanai Jarumar ta bayyana cewa masana’antar fim ta yi masu uwa ta yi masu uba shiyasa ta fito ta yi magana tun farko.
Dalili ka ga ita wannan masana’anta ta industiri mu babu abun da za mu ce da ita. Ta yi mana uwa, ta yi mana uba. Don haka da wannan abun ya zo ya faru na sarkin waka wato Naziru na fito na yi maganganu, har na fadi wasu kalma guda biyu a kanshi. ..

Saboda da na zo na fadi kalmar nan guda biyu a kan Naziru sai da na kwana ban yi bacci ba, saboda na yi mai karu. Karun nan da nayi masa sai ya zamana hankalina ya tashi sai nake ta tunani, haka na kwana ina tunani saboda ina tsoron a rayuwata ta duniya, ina tsoron ranar da zan tashi a gaban Allah da ya halicceni tunda na yi furuci wanda yana da bukatar shaidu. Don haka sai na zo da Mansura Isah dani muka je wajen sarkin waka kafin ma in je wajen shi ya ce ya yafe mun.
“Kuma kamar a kalamansa da ya yi, ba karya bane mutane da yawa, ana ta karbar kebura a nan garin, ni kaina na karbi kebura.
Naziru sarkin waka sai da ya cire mun kebura 99 a jikina. Yanzu dan Allah a samu al’ummar Annabi Muhammad SAW su dunga ragewa mutane kebura a jikinsu, wallahi komai zai warware. Yanzu misali, sarkin waka ya dauki kudi naira miliyan daya ya bani yace gas hi Fati ki je ki ja jari. Yanzu dan Allah ta yaya za a yi in manta da wannan bawan Allah a rayuwata ta duniya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA