Labarai
Nayi alƙawarin tattaki daga birnin Accra zuwa Lagos idan Super Eagles ta doke ƙasar Ghana ayau ~Cewar Jarumi, John Dumelo
Advertisment
Jarumin kaɗe-kaɗe a ƙasar Ghana mai suna John Dumelo yayi alƙawarin yin tattaki daga birnin Accra, Ghana zuwa Lagos, Nigeria idan Super Eagles ta doke ƙasar Ghana a wasan share fage na gasar Kofin Duniya da za’a fafata yau tsakanin ƙasashen biyu.
View this post on Instagram
Advertisment
Ayau ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagle zata fafata da ƙungiyar Black Stars ta ƙasar Ghana da misalin ƙarfe 8:00pm a filim wasa na Baba Yara dake Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
Shahararren jarumin, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram. Kamar yadda ya bayyana cewa, “babu yadda za’ayi Nigeria ta samu nasara a wasan yau, idan kuma suka yi nasara, zai yi tafiya ƙafa-da-ƙafa daga birnin Accra zuwa Lagos, Nigeria.