Nato ta ce ba za ta tura sojoji a yaƙin Ukraine ba
Kamar yadda anka sani fada tsakanin Kasar Ukraine da Rasha inda abun baiyi dadin ba sai yanzu nan munka samu wani rahoto kamar yadda jaridar Bbchausa ta ruwaito.
“Shugaban Nato Jens Stoltenberg, ya tattauna da manema labarai a Brussels bayan taron ministocin tsaro na ƙungiyar.
Da BBC ta tambaye shi ko akwai wasu ƙasashe da suke son a hana shawagin jirage, idan har Nato ta yanke shawarar ba za ta yi ba.
Stoltenberg ya bayar da amsa cewa mambobin ƙungiyar kansu a haɗe yake na mataki guda na kaucewa tura sojoji a ƙasa ko na sama “saboda muna da haƙƙin tabbatar da cewa yaƙin Ukraine bai fantsama ba.”
BBC ta kuma tambaye shi ko yana tunanin Ukraine ta sassuta kan burinta na shiga Nato a matsayin babban mataki na tattaunawa da Rasha.
Stoltenberg wanda yake bikin zagoyowar ranar haihuwarsa – ya ce “Ukraine ƙasa ce mai ƴanci kuma tana da damar ta zaɓi makomarta. ” Ya rage nasu su yi yanke shawarar burin shiga Nato ko kuma aa,” in ji shi.”