Kannywood

Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakaninmu – Lawan Ahmad

Shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar masana’antar, Fati Muhammad a shekarun baya.
Lawan ya ce a wancan lokacin har magana ta yi karfi tsakaninsu, domin manya sun shiga lamarin ana ta maganar aure.Na taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakaninmu – Lawan Ahmad
Sai dai kuma jarumin ya ce ana tsaka da maganar auren ne sai maganar ta wargaje domin Allah bai yi za su zama mata da miji ba. Ya kuma ce tun bayan ita bai kara soyayya da wata yar fim ba.
Jarumin ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa a wata hira a shirin ‘Daga bakin mai ita’ na BBC Hausa.
BBC ta tambaye shi ne kan ko ya taba soyayya da wata a masana’antar ta Kannywood, sai ya ce:

Mun taba soyayya da Fati Muhammad wacce har maganar aure ma ta dan shiga tsakaninmu da ita, toh amma da yake ka san komai nufi ne na Ubangiji, a wancan lokacin Allah bai yi ba. Shikenan ita ce kadai muka yi soyayya da ita, amma daga ita gaskiya ban kara soyayya da wata ‘yar fim ba.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA