Labarai

Na rubuta litattafai a kan matsalolin aure saboda lalacewar sa a cikin al’umma — Marubuciya

Aisha Aminu Ahli, wata yar kishin ƙasa wadda take jagorantar wata kungiyar dake tallafawa marayu, ta yi bikin ƙaddamar da wasu littattafai guda 2 domin ba da gudunmawa wajen taimaka wa rayuwar ma’aura, musamman a ƙasar Hausa.
Ta ce ta rubuta littattafan ne duba da yadda aure ya lalace a cikin al’ummar Hausa.

Na rubuta litattafai a kan matsalolin aure saboda lalacewar sa a cikin al'umma -- Marubuciya
Aisha Aminu Ahli

Daily Nigerian hausa ta ruwaito a zantawarta da manema labarai bayan kammala taron ƙaddamar da littattafan a yau Juma’aa Kano, Aisha tace ta rubuta littatafan ne sakamakon yadda ta ga ana samun matsaloli da yawa a gidajen ma’aurata, inda hakan ke haifar da mutuwar auren ɗungurumgum.
” Da yake akwai Kungiyar da nake jagoranta don haka Ina Samun korafe-korafe masu tarin yawa daga ma’aurata wannna tasa na fahimci akwai buƙatar na bada tawa gudunmawar wajen magance matsalolin” Inji Aisha Ahli
Aisha tace littafi na farko ta saka masa sunan “Mace-macen aure a Ƙasar Hausa; wa ke da laifi ” wanda ya kunshi abubuwan da su ke jawo matsalolin aure da kuma hanyoyin magance su.
Shi kuma dlɗayan, in ji ta, sunansa ” Sirrin kwanciyar hankali; mijinki a jakarki matar ka a aljihunka” shi kuma yana bayani ne akan rigakafin Matsalolin aure tun kafin a yi auren da Kuma bayan anyi auren.
“Ni kadai na rubuta littatafan ba tare da wani ya tallafa min ba. Sai dai na sami tallafin yan uwana da yan Kwamitin da mahaifina Allah yaji Kansa da Kuma Mijina” Inji Aisha AhliMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button