AddiniLabarai

MUSABAƘA: Gwamna Bala Ya Bada Tallafin Karatu Ga Zakarun Gasar Karatu miliyan Uku – uku

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad yace gwamnatin sa za ta ɗauki nauyin karatun zakarun gasar karatun Alƙur’ani ta kasa karo talatin da shida da ya gudana a jihar Bauchi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rufe gasar karatun a ɗakin taro na sansanin alhazan jihar Bauchi inda ya bada gudummawar naira miliyan goma ga mahalarta, miliyan goma ga zakaru da kuma miliyan biyar ga alƙalan gasar don ƙarfafa musu guiwar hidima wa littafi me tsarki.MUSABAƘA: Gwamna Bala Ya Bada Tallafin Karatu Ga Zakarun Gasar Karatu miliyan Uku - uku
Bala Muhammad yace gudanar da musabaƙar a Bauchi babbar dama da alfarma ce ga gwamnatin sa da al’umar jiha inda ya yabawa me alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’adu Abubakar kan gudummawar sa wajen tabbatar da nasarar ta.
Yayi amfani da damar wajen kira ga makaranta Alƙur’ani da su yi amfani da saƙonnin dake ƙunshe cikin sa tare da gudanar da adduo’in zaman lafiya da walwala da farfaɗowar tattalin arziki.MUSABAƘA: Gwamna Bala Ya Bada Tallafin Karatu Ga Zakarun Gasar Karatu miliyan Uku - uku
Gwamna Bala Muhammad ya yabawa jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo dake Sokoto kan shirya gasar kana yayi kira ga malaman addinin musulunci da su ƙara azamar faɗakar da al’uma da inganta tarbiyar su don kaucewa fushin Allah maɗaukakin Sarki.
Da yake yabawa Amina Idris Muhammad daga jihar Cross River, yarinya mafi ƙanƙantar shekaru cikin waɗanda suka fafata a gasar, Bala Muhammad yace shi da uwargidan sa Hajiya Aisha Bala Muhammad za su ɗauki ɗawainiyar karatun ta tare da bata tallafi na musamman don ingata rayuwar ta albarkacin littafin Allah me girma.MUSABAƘA: Gwamna Bala Ya Bada Tallafin Karatu Ga Zakarun Gasar Karatu miliyan Uku - uku MUSABAƘA: Gwamna Bala Ya Bada Tallafin Karatu Ga Zakarun Gasar Karatu miliyan Uku - uku
A nasa tsokacin, me alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar yabawa gwamnatin jihar Bauchi kan martaba mahalarta musabaƙar kana ya ja hankalin al’uma kan jin ƙai da tausayawa juna.
Sultan Abubakar sai ya kirayi ƴan Najeriya musamman ƴan kasuwa da su ƙauracewa ƙara farashin kayan abinci da na masarufi yayin da azumin watan Ramalana ke tunkarowa.

An gudanar da adduo’i na musamman yayin rufe musabaƙar da al’umar musulmi daga lunguna da saƙon Najeriya suka halarta.
Daga Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yaɗa labarai na zamani
26, Maris, 2022.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button