Addini

Muna Rokon Buhari da ya bude Rumbun abinci don rabawa talakawa – Izala

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagaoranci gagarumin taron bude babban masallacin JIBWIS a helkwatar kungiyar da ke Abuja. A matsayin babban bako a wajen bude masallacin, shugaba Buhari ya aiyana bude masallacin don fara sallah a cikin sa da sauran aiyukan ibada. A lokacin bude masallacin, shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jagoranci sallar jumma’a inda ya yi huduba da yin addu’a ga samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.
Sheikh Bala Lau wanda ya kawo tarihin gina masallacin daga gudunmawar fatun laiya da tallafin wasu bayin Allah, ya yi addu’ar rahama ga daya daga wadanda su ka tallafa da kuma ya baiyana sunan sa don Allah ya yi ma sa rasuwa wato Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba. Shehin malamin ya bukaci shugaba Buhari ya duba kara tallafawa jama’a musamman talakawa da kayan abinci don yanda a ke fama da tsadar rayuwa.
Ga bidiyon nan

Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, wasu gwamnoni da su ka hada Babagana Zulum, Umar Fintiri da Atiku Bagudu, Sanata Danjuma Goje da sauran ‘yan majalisar dattawa da shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari Kolo da sauran jama’a da dama sun shaida bude masallacin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button