Matsalar tsaron Najeriya ta gyaru – Boss Mustapha
Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce matsalar rashin tsaron da ke Najeriya ya gyaru sosai, Instablog9ja.com ta ruwaito.
Yayin jawabi a wani taro da aka yi a garin Kaduna ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, Mustapha ya ce matsalar rashin tsaron da ya yi katutu a arewa maso gabas da kuma barazanar raba kasa da kudu maso gabas suke ta yi a baya duk sun ragu.
A cewarsa, yanzu haka ‘yan ta’adda da dama mika wuya tare da tuba daga munanan ayyukan su.
Mustapha ya ce:
“Rashin tsaro ya gyaru kwarai a fadin kasar nan. Barazanar rana kasa da kudu maso gabas da kuma wani yanki na kudu-kudu suke yi ya ragu kwarai.
“Mun samu kwanciyar hankali don mun dade bamu samu rahoto akan ‘yan ta’adda sun kai farmaki wani wuri ba.
“Rundunar Operation Sharan Daji tare da taimakon jami’an rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na sirri sun taimaka wurin ganin bayan ‘yan ta’adda.”
Wannam maganar Ba gaskiya bace don kuwa mu yankin kebbi state bamajin dadi “Yan bindiga sun addabi rayuwarmu