Labarai

Maharba sun kashe wani zaki a Borno

Daraktan Gandun Daji da Namun Daji na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Borno, Peter Ayuba ya tabbatar da cewa maharba sun kashe wani zaki a Karamar Hukumar Konduga.
Da ya ke zantawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Talata a Maiduguri, Ayuba ya ce ga dukkan alamu, zakin ya kufce ne daga Gandun Namun Daji na Wazza da ke ƙasar Kamaru.
Ya ce an samu irin wannan kufcewar ta giwaye da ga gandun namun dajin, inda su ka riƙa shiga ƙauyuka kamar su Ƙaramar Hukumar Kala-Balge.
A cewar Ayuba, an samu ma kuraye sun cinye wani mutum a Ƙaramar Hukumar Kaga.
A karshe dai Ayuba ya ja kunnen mazauna yankunan da su riƙa sanya ido , inda ya ce ba abin mamaki bane zakin da a ka kashe ranar Lahadi akwai ƴan uwansa da za su iya fitowa.
A ta bakin Jami’in Yaɗa Labarai na Ƙaramar Hukumar Konduga, Asheikh Chabbol, ya ce sai da zakin ma ya tasa ƙeyar wasu masu noman rani a ƙauyen Malari, inda da ga nan ne su ka kira maharba suka harbe shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button