Labarai
LABARI MAI DADI: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Zai Rabawa Matasa Marassa Digiri 500,000 Kowannensu
Advertisment
Shugaba Muhammadu Buhari ya bada izinin sakin sama da N14 billion don horas da matasa marasa digiri 500,000 a shirin N-Power na tsawon watanni tara.
Hakan ya bayyana a zaman majalisar zartaswar tarayya FEC da shugaban ya jagoranta ranar Laraba, 23 ga Maris, 2022 a fadar shugaban kasa, Aso Villa.
Ministar jin kai da jin dadin jama’a, Hajiya Sadiya Farouq, ta bayyana hakan ga manema labarai bayan zaman kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ta yi bayanin cewa za’a yi amfani da N14 billion wajen aiki tare da hukumomin gwamnati hudu da zasu baiwa wadannan matasa horo na tsawon watanni tara.