Labarai

Kotu ta wanke matar Abdulmalik Tanko daga zargin kisan Hanifa

Yanzu nan muke samun labarin cewa wata kotun jahar kano ta wanke matar abdullahi tanko daga zargin kisan Hanifa kamar yadda freedom radio na ruwaito.Tanko

Wata kotu a nan Kano ta sallami Jamila Muhammad Sani matar Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da kashe ɗalibarsa Hanifah Abubakar.

Kotun Majistare mai Lanba 12 ƙarƙashin mai shari’a Muhammad Jibril ta wanke Jamila a zaman kotun na ranar Juma’a kan zargin da ake mata na ɓoyewa Hanifa.

Tun da fari dai Lauyan gwamnati Barista Lamiɗo Soran ɗinki ne Lauya mai gabatar da ƙara, kuma kotun ta yi la’akari da bayanan da Jamila ta bayar tare da yin nazari inda ta gano bata da wani laifi a kan batun sace Hanifa Abubakar da kuma kasheta.

Wakilin Freedom Radio ta rawaito cewa Jamila tana cike da farin ciki sakamakon wanke ta da kotun ta yi.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button