Labarai

Kotu ta tsige ƴan majalisa 20 a Cross River sabo da sun sauya sheƙa zuwa APC

A yau Litinin ne wata Babar Kotun Taraiya a Abuja ta kori ƴan majalisa 20 a Jihar Cross River sakamakon sanin sauya sheƙa da ga PDP zuwa APC.
Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya kori korafin wanda a ke ƙara na cewa ita PDP da ta shigar da ƙara, ba ta da ƴancin yin hakan.
Taiwo ya ƙara da cewa hujjar ƴan majalisan na cewa rikicin cikin gida na PDP ne ya tilasta su ka koma APC, inda ya ƙara da cewa haka wata siga ce ta yaudarar kotu.
Alkalin ya ce Abin takaici ne ƴan siyasa su riƙa banzatar da talakawa bayan sun ci zabe.
Ya ƙara da cewa ba za a ta yiwu a riƙa aikata saɓo sannan a yi tsammanin albarka za ta sauka ba.
Shari’ar ta shafi ƴan majalisar Cross River 18 da na Taraiya 2.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button