Labarai

Izala zata Bude Katafaren Massalacin data Gina da Kudin fatun Layya, da take Tarawa

Wannan shine katafaren babban masallacin juma’a Wanda kungiyar Izalah ta kasa karkashin jagoranci shugaban kungiyar Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau ya gina masallacin juma’a a babban sakateriyar kungiyar izalah dake babban birnin tarayya Abuja.
Idan Baku manta ba shekara uku kenan kungiyar Izalah ta kasa tana karban fatun layya daga hannunku a wancan shekararu ga aikin da akayi dashi wanda Gina masallacin ya lakume miliyoyin kudade masu yawa gaske.Izala zata Bude Katafaren Massalacin data Gina da Kudin fatun Layya, da take Tarawa
Ranar juma’a Mai zuwa ake sa ran Za’a bude masallacin juma’ar don cigaba da ibada a cikinsa kafin watan Ramadan insha Allah.
Allah madaukakin sarki ya sanya albarka ya kuma Kara daukaka Izalah Allah ya saka wa duk Wanda ya taimaka da gidan aljannah Amin ya Hayyu ya Qayyum.
Daga Aminu Alhaji Adamu Baushe

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button