Maigirma Mataimakin Shugaban Kasar Ghana Dr Mahmud Bawumia ya gayyaci shugaban Kungiyar Izala na duniya Ash-sheikh Dr Abdullahi Bala Lau (H) tare da Sakataren kungiyar Izala Ash-sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe (H).
Mataimakin Shugaban Kasar ya gayyaci Malaman zuwa Kasar Ghana domin su tattauna kan abinda ya shafi cigaban addinin Musulunci a nahiyar Afirka
Sannan an gayyaci Malaman zuwa kaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin kiwon lafiya wandanl aka saka mata sunan Musulunci wato Islamic Nursing Training School dake Kasar Ghana.
Kamar yadda zaku gani a hoto, ginin Makarantar yana da bene uku, bene na farko an saka sunan Kakan Ahlussunnah a Nigeria, Alqadiy Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Rahimahullah), a bene na biyu an saka sunan Sheikh Dr Kabir Haruna Gombe, a bene na uku an saka sunan Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau
Jagoran kungiyar Izala na duniya Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi alkawarin taimakawa wajen gudanar da wannan makaranta na Musulunci, sannan za’a dinga bada tallafin karatun kyauta a makarantar ma wasu dalibai masu kwazo.
Izala ikon Allah ba na mutum ba!
Yaa Allah Ka daukaka darajar Musulunci da Musulmai a duk inda suke a duniya Amin
Advertisment