Labarai

Harin jirgin ƙasa: An yi shiru na minti 1 a taron mako-mako na FEC domin karrama fasinjojin da abin ya shafa

Majalisar Zartaswa ta Tarayya, FEC, a yau Laraba a Abuja, ta yi shiru na minti ɗaya domin karrama waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.
Taron, wanda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, an fara shi ne da safiyar yau.Harin jirgin ƙasa: An yi shiru na minti 1 a taron mako-mako na FEC domin karrama fasinjojin da abin ya shafa
Daily Nigerian hausa ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shine ya yi kira da a yi shiru na minti ɗaya domin karrama waɗanda abin ya shafa.
NAN ya ruwaito cewa jirgin kasan da ya taso zuwa Kaduna, ya bar Abuja da karfe 6 na yamma a ranar Litinin, inda wasu ‘yan ta’adda da su ka kai musu hari da misalin karfe 7.45 na dare, kusan mintuna 15 kafin isowa Kaduna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button