A yau Asabar 12/03/2022 ne mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya kaddamar da kwamitin shirya gasar karatun Alkur’ani na kasa karo na 36 mai mambobi 57 da Za’ayi a jihar Bauchi.
Da yake jawabi a dakin taro na Banquet Hall dake gidan gwamnatin jihar Bauchi, Gwamna Bala ya yaba da zaben da komitin shiya gasar na ƙasa yayi ma jihar Bauchi Domin karbar bakuncin gasar karo na 36.
Ya yi nuni da cewa, gasar kur’ani wani tsari ne na horar da musulmi musamman kan karatu da haddar kur’ani mai girma da tarjamarsa da kuma karfafa ma mana gwiwa kan riƙo da littafin Allah mai tsarki.
Gwamnan kuma yayi na’am da nuna jin dadinsa kan kawo gasar jihar Bauchi yanda nan take ya sanar da bayar da gudunmuwar naira miliyan 100. Ga komitin domin inganta musabakar.
ya kuma kara da cewa taron Musabaqa na kasa karo na 36 da gwamnatinsa da hadin gwiwar jami’ar Usman Danfodio Sokoto zasu tabbatar an shirya Musabaqa na kasa mafi inganci.
Gwamnan, ya kuma yaba da yanda aka zabao kwararrun ,kuma masu amana da Gaskiya cikin komitin shirya musabakar wanda muke da tabbacin za suyi abinda ya kamata.
Da yake mayar da martani, Shugaban Hukumar, Khadi Abdullahi Yakubu Marafa, ya nuna jin dadinsa ga yadda Gwamna Bala ya Muhimman ta lamarin tare da basu goyon baya.
Ya kuma yi alkawarin tabbatar da adalci domin samun nasarar musabakar da Za’ayi a jihar Bauchi.
Lawal Muazu Bauchi
Mai Taimakawa Gwamnan jihar Bauchi kan Sabbin Kafafen Yada Labarai na zamani 12/03/02
Leave Comment Here