Addini

Don guje wa barna, iyaye su daina yi wa yaransu aure gab da watan Ramadan – Sheikh Abdallah Gadon Kaya


Babban limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya a Jihar Kano, Dr Abdallah Usman Umar, ya ce don gujewa barna barna tsakanin sabbin ma’aurata, ya kamata a tsagaita daga yin aure idan ana saura mako daya azumi.
A cewarsa, ko da kuwa auren ya matso, zai fi dacewa a kai shi can gaba, zuwa bayan watan azumin, Dala FM ta ruwaito.

Ya yi wannan bayanin ne a wani shiri na Rayuwa Abar Koyi, wanda gidan rediyon Dala FM, Kano, ya shirya wanda suke yi a duk ranar Juma’a da misalin karfe 9 na safe.
Kamar yadda ya shaida:

“Amare da angwaye ya kamara su guji yin aure kafin watan Ramadan don gudun fadawa tarkon shaidan da kuma aikata barna ta hanyar karya azumi.”

Ya ci gaba da cewa:

“Dayawan masu sabbin aure suna zuwa wuri na neman fatawa saboda sun karya a azumi a cikin watan Ramadan.”

Hakan yasa ya ja kunnen iyaye da su kiyaye aurar da yaransu aka gab da watan Ramadan, musamman ana saura mako daya.

Ya kamata masu aure su dinga fita cin Shawarma da Pizza da matansu, Dr Abdallah Gadon Kaya

Dr Abdallah Usman Umar, limamin masallacin Usman Bin Affan da ke Unguwar Gadon Kaya, ya ce ya kamata magidanta su dinga fita tare da matansu zuwa wurin cin abinci don hakan ya na kara dankon soyayya sannan kuma kyautatawa ce ta masoya. labarunhausa na ruwaito
Dakta Abdallah ya kara da cewa idan namiji yana yin hakan zai kara shakuwa tsakaninsa da matarsa.

Ya shaida hakan ne a wani shiri na Dala FM na Rayuwa Abar Koyi da ya gudanar a ranar Juma’a.
Kamar yadda yace:

“Magidanci zai samu shakuwa da kyautatawa tsakaninsa da matarsa idan har yana fita tare da ita zuwa wurin cin abinc

tare da zagawa da ita cikin gari musamman wuraren da bata sani ba.”

Ya kara da cewa:

“Bai kamata mazajen aure su dinga yin saurin fushi tsakaninsu da matansu ba, ya kamata su dinga hakuri maimakon yin hakan.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button