Labarai

Da Dumi Dumi : Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kudirin Baiwa Dukkannin Kananan Hukumomin Najeriya Cin Gashin Kai

Kudirin bayar da cikakken ikon cin gashin kai na kudi da na mulki ga kananan hukumomi, Majalisar Dattawa ta zartar da su.
Kudirin dai na neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasa domin soke asusun hadin gwiwa na kananan hukumomin jihar da kuma samar da wani asusu na musamman inda za a biya duk wani kason da ya kamata na kananan hukumomi, daga asusun tarayya da na jiha.Da Dumi Dumi :  Majalisar Dattijai Ta Amince Da Kudirin Baiwa Dukkannin Kananan Hukumomin Najeriya Cin Gashin Kai
A cikin kudirin dokar, kowace karamar hukuma za ta kirkiri tare da kula da asusunta na musamman da za a kira Local Government Allocation Account wanda za a biya dukkan kudaden da aka ware a cikinsa.
Dokokin sun kuma umurci kowace jiha ta biya kananan hukumomin da ke yankinta na kudaden shigar da take samu a cikin wadannan sharuddan da kuma yadda majalisar ta tsara.
Domin samun ‘yancin cin gashin kai, kudirin na neman baiwa kananan hukumomi damar gudanar da nasu zaben da kansu.
‘Yan majalisar sun kuma kada kuri’ar amincewa da ‘yancin cin gashin kan harkokin kudi ga majalisun dokokin jiha da na bangaren shari’a.
A yayin gudanar da zaben, Majalisar Dattawa ta shaida cewa sama da kuri’u 73 aka samu game da matakin da ake bukata don aiwatar da irin wadannan kudade.
Daga Comr Abba Sani Pantami

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button