Buni zai dawo kan kujerarsa ta shugabancin riƙon APC
Ga dukkan alamu, Shugaban Kwamitin Riƙo na Jam’iya mai mulki APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne zai jagoranci babban taron APC na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.
Jaridar Punch ta jiyo cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci Buni ɗin da ya jagoranci taron, amma ya masa zazzafan kashedi cewa ba za a ƙara ɗage ranar yin Babban taron jam’iyar na ƙasa ba.
Majiyoyi sun shaida wa Punch cewa Buhari ya ɗauki wannan matakin ne bayan ganawa da ya yi da wasu jiga-jigan jam’iyar a Landan.
Da ga cikin waɗanda su ka baiwa Buharin shawarar ɗaukar wannan matakin akwai Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, wanda ya nuna wa shugaban ƙasar illar da za a iya samu ta ɓangaren Shari’a.
Haka-zalika an jiyo cewa, bayan da a yanzu shugaban ƙasar ya nuna ba shi da wani ɗan takara a zaben shugaban jam’iyar na dindindin, yanzu gurbin ya zamto a bude, inda kowa zai iya nema.
Hakan kuma, in ji majiyoyi, ya nuna rashin tabbas a kan rabon muƙamai na shiyya-shiyya da jam’iyar ta fitar a makon da ya gabata.
Haka kuma a ganawar ta birnin Landan, Buhari ya musanta bada umarnin cire Buni da kuma maye gurbinsa da Gwamna Abubakar Sani Bello kamar yadda Gwamna Nasir El-Rufai ya faɗa.
– Daily Nigerian hausa