Buhari ga ƴan Nijeriya: Ina mai baku haƙuri kan wahalar mai da wutar lantarki
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa a kan halin da ƴan ƙasa su ka shiga sakamakon ƙarancin man fetur da dangogin sa da kuma wutar lantarki, inda ya ba da haƙuri game da yanayin da a ke ciki.
Buhari ya bada hakurin ne a sanarwar da kakakin sa, Garba Shehu ya fitar a jiya Laraba.
Buhari ya ce matsalar man fetur da dangogin sa, matsala ce da gwamnatin sa ta magance tsawon shekaru bakwai a ƙasar nan.
Sai dai kuma Shugaban ya tabbatar da cewa nan ba da daɗewa ba wannan matsala ta man fetur da wutar lantarki za ta zama tarihi kamar yadda jaridar daily Nigeria ta ruwaito
Ya ce” gwamnatin mu na da masaniyar cewa ƙarancin man fetur da dangogin sa da wutar lantarki ya haifar da naƙasu a kan rayuwar ƴan ƙasa da kasuwanci, amma kuma sauki na nan tafe.
“Ina mai baiwa kowa da ko ina a ƙasar nan hakuri.
“Gwamnati na aiki dare da rana domin magance wannan matsala. An Fara gudanar da kundin gyaran matsalar man fetur ɗin kuma mu na fatan za a samu nasara,”