Kannywood

[Bidiyo] Kashe Ahmad S nuhu ankayi ba Mutuwar Allah bace nima Allah ne ya kwace Ni – inji Safiya musa

Tsahar tsakar gida ta wallafa wannan labarin inda take cewa wani video da muka ci karo da shi a shafin media hausada suka kwafo daga shafin titkok na tsohuwar jarumar masana’antar kannywood safiya musa ya bayyana cewa wani sirri da duniya bata sani ba game da mutuwar jarumi margayi ahmad s Nuhu inda take bayyana kashe shi akayi ba mutuwar Allah da annabi bace dukda kwana sun kare.

A cikin bidiyon safiya Musa ta bayyana yadda anka basu maƙudan kuɗaɗe da zummar zasu je Maiduguri gala Ahmad s Nuhu an bashi N500k ita an bata N700k inda ganin yawan kudin yasa ita ta karbi dubu N20k kawai tace bazaje ba ta bayan tafiyar sai ji kawai tayi Ahmad s nuhu yayi hatsari ya mutu wanda tace da taje da itama ta mutu ko ta sha wahala.

Sai dai a cikin bidiyon bata bayyana wanda take zargi da kashe Ahmad s Nuhu ba kuma bata kuma bayyana ta hana ahmad s Nuhu hana ahmad s nuhu ba kamar yadda a labarin aka kira ya mutu batayi mamaki ba.

Koda yake cikin hamzari take bada labarin kuma ana ta kiranta ana cewa ta bar maganar jama’a suna jinta wanda har kiranta aka yi a waya ana ce mata ta bar maganar amma sai da ta kai aya..

Shin Miyasa Safiya Musa taba fadi Wannan Maganar ba sai yanzu?

Bamu san dalilin da yasa safiya Musa bata fito da wannan maganar ba tsawon shekaru da goma sha biyar ba sai yau duk da tasan magana ce da zata iya tada hankalin ko hukuma da yan uwan mamacin su ce zasu karkade file su cigaba da bincike wanda dole hana zai sa su jin karin bayani daga dare ta.
Daga karshe tsohuwar jarumar tayi addu’a Allah ya gyara industiri din in kuma baza ta gyaru ba Allah ya tarwatsa ta tsirarun da suka rage su gyara su amfana ga videon hirar da akayi da safiya Musa a live dinta na titkok.

 

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button