Labarai

[Bidiyo A] Abin kunya ne na yi bara – inji Makaho mai niƙa a Oyo

Advertisment

Wani bawan Allah mai suna Muhammad sa’adu mazauni a jihar oyo wanda jaridar Aminiya sunkayi hira da shi wanda labarin wannan bawan Allah akwai sha’awa sosai wanda baida matattar zuciya.
Muhammad sa’adu yace wannan al’amarin ya same shi yana dan shekara 30 a lokacin a kwana a tashi kawai ciwon yana ta tafiya sun nemi maganin gargajiya sunsa baiyi ba sun nemi na turawa shima baiyi ba sun je wata assibiti da ke jihar Kano akace idonsa ya lalace yace to shikenan ya dogara ga Allah.
Muhammad Sa’ad yace daman shi yana gyaran rediyo inda yayi zama a legas saboda rashin ido ya sameshi ya daina gyaran rediyo ya koma zama a gida.
Shine mutane suke zuwa suna bashi wani abu domin yaci abinci ga nan suke ce yaje yayi bara.
Sai yace” auzubillahi minna shedani rajim yace a’a baiyi bazai iya ba.”
Muhammad Sa’ad yace shi ɗan jinin sarauta ne aganshi yana bara abin kunya ne saboda haka ba zaiyi bara ba.
Muhammad ya bayyana cewa ƙanensa ne ya sayo injimi sai ya baiwa wasu yaransa suna niƙa basa kawo kudi sai su kashe a ranar yazo nayini dasu nagaji naga yadda suke aikin sai kawai washe gari sun watse anka kawo niƙa sai na tada innji nayi niƙa lafiya lau.
Muhammad ya bayyana cewa yanzu yakai shekara goma sha biyar yana niƙa kuma bisa ikon Allah haryanzu babu abinda ya same shi.
Ga bidiyon nan kasa ku kalla.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button