Kannywood
Bashir Mai Shadda ya bayyana Gaskiyar zance Aurensa da Jaruma hassana Muhammad
Advertisment
Fitaccen mai shirya Finafinan Hausa Abubakar Bashir Abdulkareem, wanda aka fi sani da ‘Mai Shadda’ zai angwance da Amaryar sa Hassana Muhammad a ranar Asabar, 13 ga watan Maris 2022.
Hassana Muhammad, wadda ita ma jarumar Finafinan Hausa ce, sun share akalla kusan shekaru biyar suna soyayya da Mai Shadda, daga baya kuma Mai Shadda din ne ya hanata fitowa a Finafinai kwata-kwata.
A yanzu haka dai za a iya cewa karshen Tika-Tika Tik.
View this post on Instagram
Sai dai Mai Shadda, ya ba wa da yawa daga cikin mabiyansa kafa, sakamakon wani hoton da ya wallafa tare da Aisha Muhammad Idris (Ayshatul Humaira) wanda a cewar sa zai yi wuf da ita.