Labarai

Bashin da a ke bin Nijeriya zai kai Tiriliyon 45 a shekarar 2022, in ji DMO

Ofishin Kula da Basussuka, DMO, ya ce akwai yiyuwar yawan basussukan da a ke bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 45 a shekarar 2022 da mu ke ciki,kamar yadda daily Nigeria hausa na ruwaito
Wannan bayanin ya zo ne a yayin da gwamnati ke shirin ƙara ciyo bashin Naira tiriliyan 6.39 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2022.
Patience Oniha, Darakta-Janar ta DMO ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a yau ranar Alhamis a Legas, yayin da take magana a kan wani shiri na wayar da kan jama’a da ofishinta ya shirya.
Oniha ta bayyana cewa gibin kasafin kudin na shekarar 2022 ya kai Naira tiriliyan 6.30, wanda yai daidai da kashi 3.46 na GDP na kasar.
Ta ce, sai an ciyo bashi a gida da waje da kuma kuɗaɗen da a ka samu wajen jimginar da kadaroein gwamnati sannan za a iya cike giɓin kasafin kudin.
“Kimanin Naira Tiriliyan 2.57 za su fito daga gida, Naira Tiriliyan 2.57 daga kasashen waje, Naira Tiriliyan 1.16 daga raguwar lamuni da aka samu tsakanin bangarorin biyu da kuma Naira Biliyan 90.7 daga kudaden da ake samu daga hannun jari,” inji ta.
Sai dai kuma ta ce ciyo bashin kuɗaɗe domin cike giɓin kasafin kudi da samar da gine-gine da ababen more rayuwa ba abu bane maras kyau.
Oniha ta ƙara da cewa gwamnatocin ƙasashen duniya na ranto kuɗaɗe domin yin Aiyukan ci gaba a kasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button