Labarai

Ban Yi Ma PDP Adalci Ba Da Na Yi Waƙar Shegiyar Uwa – Haruna Aliyu Ningi

Shahararren mawaƙin siyasar nan mai suna Haruna Aliyu Ningi ya ce, bai yi ma jam’iyyar PDP Adalci ba da ya wakar da ya kira ta da ashegiyar uwa.
Haruna Ningi ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Ningi ya ce a da a zatonshi matsalar Najeriya matsala ce da jam’iyya to sai daga baya ya gano ashe matsalar shuwagabanni ne.
Mawaƙin har ya bada misali da cewa a shekarun baya sun ta kiran mutane da nuna masu su zo a yi APC to amma yanzu daga baya ya gane abin ba haka ya ke ba.
Ya ƙara da cewa yanzu haka yana da wani da ke son takara da yake goyon bayansa a jam’iyyar ta PDP.
“A cikin amshin waƙar da Ningi yayi ma PDP dai yana cewa “Shegiyar uwa mai kashe ƴaƴanta PDP ƴan ƙasarmu ba mai daɗa binta tunda mun farga” ya ce a cikin waƙar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA