Kannywood

Babu abinda ke sanya ni baƙin ciki irin na tuna zan mutu in koma ga Allah – Maryam yahaya

Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Yahaya yayin zantawa da BBC Hausa ya shaida cewa babu abinda ya fi bakanta mata rai kamar ta tuna cewa watarana zata mutu ta tarar da Allah.

Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne jarumar ta yi wani gagarumin ciwo wanda yasa ta fita daga hayyacin ta har wasu suka dinga tunanin mutuwa zata yi.
Babu abinda yake sa ni bakin ciki kamar in na tuna zan mutu in tarar da Allah, Jaruma Maryama Yahaya.

Ciwon ya yi matukar sauya mata halitta har ta kai ga wadanda suka san ta basa gane ta, yanzu haka dai ta warke sarai tamkar bata taba ciwo ba.
A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris a wani bidiyo wanda BBC Hausa ta wallafa na tattaunawar da aka yi da ita ta bayar da takaitaccen tarihin ta.shafin labarunhausa ta tattacen kadan daga cikin tambayoyin.
Kamar yadda tace:

Ni dai sunana Maryam Yahaya, an haife ni a garin Kano, Anguwar Goron Dutse.”

Ta ci gaba da cewa ta yi karatun firamare da sakandare, sannan tun tana karama ta ke sha’awar fara fim wanda yanzu haka take gode wa Allah akan fim din da ta ke yi.

Ta ce ta fara fim a shekarar 2016 wanda ta fara da fim.

din ‘Masoor’ kuma a yanzu haka bata san yawan fina-finan da ta yi ba kuma duk tana son su sosai.

Yayin da aka tambaye ta abinda yake sa ta farin ciki cewa ta yi:

Gaskiya abinda ya ke sa ni farin ciki abu ne guda daya. Babu abunda yake saka ni farin ciki kamar in ga iyaye na da ‘yan uwa na cikin farin ciki.”

Yayin da aka tambaye ta abinda yake saka ta bakin ciki sai ta kada baki tace:

“Babu abunda yake saka ni bakin ciki irin in tuna cewa wata rana zan mutu in koma ga Ubangiji na.”

Dangane da abincin da ta fi so ta ce Tuwo miyar kubewa danya, kuma ta ce bata da babbar kawa a Kannywood, mahaifiyar ta ce babbar kawar ta.

Ta ce a Kannywood tana da yayyi mata, iyaye da kuma kawaye masu ba ta shawara.

Ta ce kasashen da ta taba zuwa sun hada da Saudiyya, Dubai, Gambia, Nijar da sauran su.

Ta ce tana burin ta rabu lafiya da duk ‘yan Kannywood ta kuma yi aure. Kuma tana da burin yin siyasa.

Ga hirar bidiyon kasaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button