Kannywood

Auren Zarah Diamond ya mutu bayan watanni 7

Tashar Tsakar Gida ta bayyana yadda suka samu labari akan mutuwar auren da Zara Diamond ta yi a sirri a watanni 6 zuwa 7 da suka gabata kamar yadda labarunhausa na bayyana
Kenan ta bi sahun su Rahama Hassan, Hafsat Shehu da su Mansura Isah.
Tsawon lokaci kenan da Zara Diamond ta bude shafukan sada zumunta na Instagram da TikTok inda take wallafe-wallafen ta cike da nishadi.
A kwanakin nan ne abubuwa suka sauya salo don a lokacin da ta yi auren sirri ta goge duk wasu shafukanta na kafafen sada zumunta kuma ta bukaci shafukan masoyanta wato Fan Page da su goge don ta yi aure.
Tun bayan auren ta, ba a fiye ganin jarumar ba sai a kwanakin nan da abubuwa suka sauya inda ake ganin tana bidiyo da kananun kaya kuma babu dankwali akanta.
Wannan sauyin yasa mutane suka fara sanya alamun tambaya domin lamarin da mamaki, don ko hoto ta daina wallafawa ballantana batun bidiyo.
Wata majiya ta tabbatar wa Tashar Tsakar Gida cewa tabbas aurenta ya dan jima da mutuwa sai dai bata riga ta bayyana bane.
Hakan yasa Tashar Tsakar Gida ta tuntubi wani furodusa da ke da alaka da ita, Sunusi Multimedia don ya bayar da lambar wayanta a ji daga bakin ta.Auren Zarah Diamond ya mutu bayan watanni 7
Sai dai ta tura sako cewa a lokacin da zata yi auren ta babu wani dan jarida da ta tuntuba, don haka bata ga dalilin da zai sa a dame tada tambayar auren ta ya mutu ko kuma bai mutu ba.
Da fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, Ameen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button