Labarai

Auren dole : Budurwa Ta kashe Kanta a Ranar Aurenta a kano

Wata Budurwa ta Kashe kanta Sanadiyyar shan guba a cikin Abinci a Ranar Alhamis a garin Agalawar Balan da ke Karamar Hukumar kabo A jihar Kano, shafin Rigar Yanci International a Facebook sunka wallafa
Budurwar Mai suna Zainab ta dauki wannan matakin ne Saboda kin ba ta saurayin da ta ke ƙauna a matsayin Miji inda a ka Ɗaura mata Aure da Wanda ba ta So.
A Tattaunawar da wakilinmu Yayi da Ado mai Niƙa maƙwabcin garin ya shaida Mana Cewa Zainab Ta sha gubar ne Saboda ba ta son saurayin da Iyayenta suka ɗaura mata Aure da Shi.
A wani Bangare Guda Kuma an ce kawar Amaryar ita ce ta sakawa Amaryar guba a cikin Abinci Saboda bakin cikin kawarta Zainab Ta samu miji ita Ba ta samu ba tuni dai a ka nemi kawar amaryar a ka rasa ta gudu Daga garin zuwa wani wuri wanda ba a sani ba.
Duk da dai Dagacin garin ya dauki matakin kashe maganar A cikin Gida hakan ya sa suka ƙi Sanar da Jami’an tsaro amma Yanzu dai Maganar ta kai ga Ƙungiyar Rigar Yanci International ta tsoma baki.
Yanzu haka dai Ƙungiyar mai Rajin Kare Haƙƙin Bil’adama Ta Ƙasa Ƙarƙashin Jagorancin Shugabanta na Jihar Kano Kwamared Usman A Usman ta ce ta duƙufa Dan gano Sahihin abin da ya faru tare da miƙa batun zuwa ga Manta Sabo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button