Labarai

Ƴan sanda na farautar makusancin Shekarau, Bashir Gentile a Kano

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano na shirin cafke wani shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa, Bashir Gentile, a kan zargin sukar gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, a wasu shirye-shiryen rediyo, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito.
Bashir Gentile dai na hannun dama ne ga tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, kuma mai taimaka wa shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a halin yanzu.
Jaridar ta rawaito cewa bayan yunkurin kama Gentile ya ci tura, a yanzu rundunar ƴan sandan ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi kan karar da aka shigar a kansa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce ba shi da masaniya a kan gayyata ko shirin kama Bashir Gentilen.
Sai dai kuma SP Kiyawa, ya ce zai kara yin bincike kan lamarin.
A baya-bayan nan dai da dama daga cikin masu sukar gwamnan suna fuskantar tuhuma a gaban Alkalai bayan ‘yan sanda sun kama su.
Da ga cikin masu sukar gwamnatin da a ka cafke sun haɗa da Muaz Magaji da kuma Abdulmajid Danbilki Kwamanda, wanda a halin yanzu ya na gidan yari, sakamakon kasa cika sharuɗɗan beli da a ka gindaya masa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button