Ɗan lelen Buhari, Abdullahi Adamu ya zama Shugaban jami’yar APC
Tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu, ya zama sabon zababben Shugaban Jami’ya mai Mulki ta APC na ƙasa.
Adamu, wanda shine Sanata mai wakiltar Nassarawa ta Yamma, ya zama shugaban jami’yar na ƙasa tun bayan da a ka rushe shugabancin Adams Oshiomole, shekara ɗaya da wata tara da ya gabata.
An zaɓi Sanata Adamu ne ta hanyar maslaha, inda dukka ƴan takarar kujerar su ka janye masa a wajen Babban Taron APC da ya gudana a dandalin Eagle Square a Abuja a jiya Asabar.
Tun tuni dai Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna wa kusoshin jam’iyar cewa shi Sanata Adamu ne ɗan takarar sa na shugabancin jam’iyar a matakin ƙasa.
Tuni kuma gwamnonin APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar su ka amince da buƙatar ta Buhari.
Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓen, shi ya sanar da Sanata Adamu a matsayin shugaban jami’ya na ƙasa bayan da duk kusoshin jam’iyar da nasu ruwa da tsaki sun amince.
Sources : Daily Nigerian hausa