Labarai

Ƴan bindiga sun sace fasinjoji da dama bayan sun kai hari kan jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace wasu fasinjoji da ba a bayyana adadinsu ba daga wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin.
Shaidu sun ce jirgin ya kauce daga kan hanyarsa bayan fashewar wani abu a kan hanyarsa.
Rahotanin sun ce an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata.An kai wa jirgin kasan mai dauke da fasinjoji kusan 1,000, harin ne da misalin karfe 8 na dare.Yan bindiga sun sace fasinjoji da dama bayan sun kai hari kan jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Fasinjoji da kuma ‘yan uwan wasu fasinjojin sun shaida wa BBC cewa lamarin ya yi matukar muni kuma har yazu ba a san takamaiman mutanen da lamarin ya shafa ba.
Wani fasinja ya shaida mana cewa bayan jirgin ya tsaya, ‘yan bindiga sun kewaye shi tare da bude wuta.
Mutane sun sunkuya kasa domin samun mafaka kuma daga nan ne maharan suka nufi hanyar jirgin, inda suka harbe fasinja daya a kusa da inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, in ji shi.
Muna cikin tafiya kawai muka ji abu ya yi kara, bam ya tashi ya girgiza sannan kuma muka ji karar harbe-harbe, bayan an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ke cikin jirgin Allah ya taimake mu jami’an tsaron sun fi karfin su amma duk da haka sun kwashi wasu mutane a ciki”, a cewar sa.
Wani fasinjan da ke cikin jirgin ya ce an samu asarar rayuka.
Ya ce sun kashe mutum guda. “Mun ji ƙarar harbe-harbe, muna cikin tashin hankali,” in ji shi.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an tura sojoji domin ceto fasinjojin tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Yawaitar kai hare-hare da sace-sacen mutane da ake yi a babban titin Abuja da Kaduna ce ta sa matafiya da yawa suka gwammace yin tafiya ta jirgin kasa.
Sai dai wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari kan hanyar jirgin cikin watanni shida da suka wuce.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button