Labarai

Ƙungiyar Miyetti Allah Ta Koka Kan Zargin Kashe Ma Ƴaƴanta Shanu A Jahar Filato

Kungiyar Miyetti Allah ta yi zargin cewa da alamu an bullo da wani sabon salon kashe shanun ‘ya’yan ta a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Shugaban kungiyar na karamar hukumar, Ya’u Idris, ya yi wannan zargi a cikin wata hirar da ya yi da manema labaru da yammacin ranar Litinin.
Ya ce makiyaya sun rasa shanu sama da ashirin a yankin a cikin wannan wata na Maris inda ya yi zargin cewa ana sanya gubar ne a cikin ruwan da dabbobin ke sha da kuma ‘yayan mangwaron da akan zubar a kasa domin shanun su ci.
Idris ya ce, binciken likitocin dabbobi ya nuna guba ce ta hallaka shanun da aka yi wa gwajin gano musabbabin mutuwar su, sannan ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakin da ya dace da nufin hana sake tashin rikicin manoma da makiyaya a yankin da jihar baki daya.
Jakadiyar RTV ta ruwaito cewa ya zuwa yanzun dai ba a ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato din ba dangane da lamarin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button