Labarai

Ƙungiyar mata Musulmi sun baiwa Abba K. Yusuf lambar yabo ta zaman lafiya

Wata ƙungiya mai suna Initiative for Muslim Women in Nigeria, da ke da shelkwata a Jihar Kaduna ta karrama ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyar PDP a zaben 2019 Engr. Abba Kabiru Yusuf, bisa gudunmawar da ya ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya a jihar.
Wannan na ƙunshe ne s wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam ya fitar a yau Lahadi.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-Gida, ya samu ƙuri’u mafi rinjaye a zaɓen gwamna wanda aka yi a ranar 9 ga watan Maris 2019, amma sai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Ƙungiyar mata Musulmi sun baiwa Abba K. Yusuf lambar yabo ta zaman lafiya
Ƙungiyar mata Musulmi sun baiwa Abba K. Yusuf lambar yabo ta zaman lafiya

A cewar ƙungiyar, ta baiwa Abba Gida-Gida lambar yabon ne sabo da ƙoƙarin da ya yi na ganin ba a samu wani tashin hankali a Kano ba bayan ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, duk kuwa da ɗumbin al’ummar da ya ke da su.
Wannan ne ya sanya ƙungiyar ta ayyana Abba Gida-Gida a matsayin jakadan zaman lafiya saboda gudunmawar da ya ke bayarwa wajen zaman lafiya.
A lokacin da take jawabi ya yin bikin karramawar, shugabar ƙungiyar ta bayyana cewa, an ba shi lambar yabon ne saboda cancantar da ya yi, ba don wani dalili na siyasa ba.
Ta ce “Abba Gida- Gida ya cancanci a yaba masa, saboda abun da yayi na tabbatar da cewa Kano ta ci gaba da zaman lafiya, duk da sabanin siyasa da ake fama da shi tsakanin sa da abokin takarar sa,” in ji ta.
A jawabinsa a yayin taron, Yusuf, wanda Dr. Faruk Kurawa ya wakilta, ya godewa kungiyar bisa wannan karramawar tare da jaddada aniyar sa, na cigaba da bayar da duk wani goyon bayan da ya dace domin zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Kano da ma Nijeriya baki daya.
“A matsayina na dan siyasa nagari, uba kuma kaka, a shirye nake a koyaushe in sadaukar da rayuwata domin samun zaman lafiya, babu wata al’umma da za ta iya cimma burinta ba tare da zaman lafiya ba,”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button