Addini

Zan Iya Shafa Magani Saboda Gemu Ya fito? – Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Zan Iya Shafa Magani Saboda Gemu Ya fito? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*
Assalamu Alaikum Allah ya qarawa Dr lapia ina da tambaya :
Shin ya halatta mutum ya shafa cream, domin gemunsa ya fita Ya tsayar da SUNNAH ?

*Amsa*

wa alaikum Assalam, Zai fi kyau ya jira har Allah ya fito masa da shi, saboda amfani da magungunan da suke canza yanayin dan’adam yana biyar da matsaloli a mafi yawan lokuta.

Allah yana iya ba ka ladan wanda ya tsayar da gemu ko da bai fito ba, mutukar niyyarka ingantacciyya ce.
Allah ne mafi sani
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
24/01/2022

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button