Zamana matar Adam A zango ya jawomin koma baya -Inji tsohuwar matarsa Amina Rani
Kamar yadda Jaridar ta wallafa bidiyon tattaunawar da ta yi da ita a Facebook ranar Asabar, tace akwai wasu furodusoshi da suke mutunci da Zango kuma suna ganin idan sun sa ta a fim dinsu zai janyo musu matsala da shi.
Amma ta ce ita dai ta san tana son ta yi suna da kanta. Ta kara da shaida yadda ta tsinci kanta a harkar fim din inda ta ce:
“Eh to, bayan na gama makarantar sakandare, Allah ya ji kan Ahmed S. Nuhu, lokacin na san shi, da shi na fara haduwa har muka yi dan wani fim, sai abin ya zo daidai da zan yi aure, sai ba a saki fim din ba sanadiyyar zan auri dan fim. Amma bayan nan ban wani nuna ra’ayin fim ba. Sai daga baya a hankali-a hankali na fara jin ra’ayin ina so in koma harkar fim.”
Advertisment
Ta bayyana yadda ta fito a wani fim mai suna “Gidan Mai Shayi” na Sani Danja wanda aka yi a garin Kaduna. Bayan nan ta yi ‘Gidan Danja’.
Yayin da aka tambayeta idan zama matar Adam Zango ya taimaka mata, cewa ta yi:
“A zama na tsohuwar matar Adam A. Zango, zan iya cewa daga farko ya dan ja ni baya. Saboda wasu furodusoshi da sauran su, suna ganin suna mutunci da shi suna tare da shi, suna ganin kamar idan suka sa ni a fim zai iya kawo musu matsala da shi da sauran su. Amma ni dai abinda na sani shi ne ina so in nema wa kaina suna, ba wai sai don Adam A. Zango ba, saboda ina da abubuwa da yawa da zan ba industiri, na san akwai abubuwan da zan iya yi.
Ta yi bayani akan yadda mutane suka dinga cece-kuce bayan ta wallafa hoton Adam Zango domin yi masa murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Jaridar labarunhausa tayi kokarin tattara bayyanai ,a cewarta akwai mutunci da kuma da a tsakanin su don haka ba ta tunanin akwai damuwa don ta yi hakan. Ta ce shi ne mutum na farko da ta fara tuntuba ta sanar wa kudirinta na komawa fim har ya bata shawarwari.
Ta kara da bayyana kudirin ta na zama babbar darekta mace kuma fitacciya. Daga karshe ta yi wa masoyan ta fatan alheri.