Labarai

Yanzu – Yanzu : Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama Abba Kyari

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama Abba KyariRahotanni daga Najeriya na cewa rundunar ƴan sandan ƙasar ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari.
Rahotannin sun ce a yanzu haka ana tsare shi a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.

Bbchausa ta ruwaito Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan kasar ba ta fitar da sanarwa kan batun ba.

 

A ranar Litinin ne hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

  1. A gaskiya rundunar ‘yansada a nigeria tana iya bakin kokarinta domin duk wani mai laifi a nigeria koshi wayene ta kamashi ayi binchike akansa duk matsayinsa sannan kotu kuma tayimasa hukunci dai dai da laifinsa ,l love my country nigeria I’M from YOBE STATE L,G,A YUSUFARI

  2. Agaskiya bana tunanin zargin da akewa abba kyari yazama gaskiya duda cewa dan adam ajizine amma allah yana tare da mai gaskiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA