Labarai

‘Yan Kasuwa Na Cin Ribar N1,000 A Kan Kowane Buhun Siminti – Kamfanin BUA

Kamfanin sarrafa siminti na BUA, ya zargi ’yan kasuwa da cewa su ne kanwa uwar gamin da suka sa farashinsa ya ki saukowa a Najeriya aminiya ta ruwaito.

Abdussamad Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanin BUA
Abdussamad Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanin BUA

A cewar kamfanin, ’yan kasuwar ne suka hana farashin saukowa, duk kuwa da ragin kaso 10 cikin 100 da ya yi a kan farashin kowane buhu.
Shugaban kamfanin, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u ne ya bayyana haka a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan da kammala ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.
Ya ce tuni kamfanin nasa ya fara tattaunawa da sauran masu sarrafa simintin da nufin ganin an rage farashinsa a Najeriya.
Sai dai ya ce, “Muddin ba mu samu hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ba, to ba za a ga tasirin yunkurin namu ba.
“A zahirin gaskiya, mun yi tunanin bayan mun rage farashin simintinmu da N350, sauran kamfanoni za su bi sahunmu, amma sai suka ki.
“Mun kuma ga yadda farashin ya ci gaba da karuwa, lamarin da ya sa manya da kananan diloli kan samu ribar kusan N800 zuwa N1,000 a kan kowane buhu,” inji Abdussamad.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Duk wanda ya tsanantawa al’ummar kasarmu nigeria da abinda al’ummar ke amfana dashi
    Shima Allah ya tsananta masa ko menene inji fiyayyen halitta Annabi muhammad saw kuma addu’ah ta karbu ga duk wanda hakan ta faru dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA