Kannywood

Wani Hadisin Annabi Muhammadu S.A.W na tuna, shiyasa na ba Fati Slow N1m – Naziru Sarkin Waka

Advertisment

Wani Hadisin Annabi Muhammadu S.A.W na tuna, shiyasa na ba Fati Slow N1m, Inji Naziru Sarkin WakaAlhaji Naziru Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya bayyana dalilin da ya sa ya maida sharri da alheri.
Fitaccen mawakin yake cewa ya tashi daga barci sai ya ji ana ta magana a game da kalaman da Fati Slo tayi, har ana ba shi shawarar ya kai kara.
Mawakin ya bayyana cewa abokansa da suke aikin lauya sun yi masa maganar cewa a shiga kotu. An wallafa bidiyon hirar a shafin Facebook.
A nan ne sai ya ce wani hadisin Manzon Allah Muhammad (SAW), ya bijiro masa, wanda da shi ya yi amfani, ya ba jarumar wasan kwaikwayon kyauta. Gundarin wannan hadisi na Annabi SAW yana cewa:
“Ku ji tsoron Allah SWT a duk inda ku ka samu kan ku, ku biyo aikin sharri da na alheri, na alherin zai shafe sharrin, ku mu’amulanci mutane da kyakkyawan dabi’a.”
Abu Dharr da Mu’adh Jabal suka ji wannan hadisi daga bakin Annabi SAW. Tirmidhi ya inganta hadisin a littafinsa.


Abin mamaki, bayan Nazir Ahmed ya cika alkawarin da ya yi wa tauraruwar, sai aka ji ta fito fili ta na ba shi hakuri a kan laifin da ta yi masa a baya.
An gayyaci mawakin ne a shirin AmonGaskiya wanda aka saba yi a wannan gidan talabijin.
Daga Ahmad Aminu Kado.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Ashe Kasan abinda kayi ba dai dai bane kenan, domin wannan hadisi Yana magana akan idan ka aikata munanan aiyuka kabisu da yayyafin kyawawa neh…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button