Tabarakallah : Sarkin waka ya turawa Ladin cima Naira miliyan 2 kamar yadda yayi Alkawali
Inda a cikin wajen martani na bbchausa ali nuhu ya musanta maganar ladin cima na cewa batayi musu adalci ba tace wai dubu biyu 2 dubu 5 sune ake biyata.
Wanda maganar falalu dorayi da ali nuhu sunka fusata sarkin waka nazir m ahmad ya fito yayi musu wankin babban bargo akan cewa babu tsoron Allah a cikin zukatansu to a nan fa anka fara musayar yawo a masana’antar.
Amma daga baya ya fito ya baiwa kowa hakuri da nuna cewa baiyi dan wani yaji haushin ba suyi hakuri.
Nan ne yace idan har na abinci ne ke kawo ladin cima mama tambaya a masana’antar kannywood zai bata miliyan biyu ta ja jari.
To Alhamdulillahi wannan shine risit na cewa an turawa ladin cima naira miliyan biyu a asusun bankinta.