Labarai

Taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran ƙasashe

1.0 Gabatarwa
Duk wani dattijon da bai wuce shekaru 70 ba, to haƙiƙa ba shi labarin abun da ya faru a Yaƙin Duniya I da II aka yi, to ballantana kuma matashin da bai wuce 40 ba, ko kuma mu jarirai. Don haka ba mu san yaƙi ba, kuma ba mu san wace illa yake tattare da shi ba. Amma duk wanda ya amsa sunansa “mutum” da ke rayuwa a gabas-maso-arewacin Nigeria, to haƙiƙa ya san “yaƙi” walau kai-tsaye ko ta bayan fage.Taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran ƙasashe
An yi Yaƙin Duniya I daga shekarar 1914-1918, an yi na II daga 1939-1945; Ɗan Adam ya kalli tashin hankalin da bai taɓa gani ba, an kashe miliyoyin mutane, an karya tattalin arziƙin duniya, an wahalar da na wahalarwa, an kashe na kashewa, an kuma durƙusar da na durƙusarwa. Haƙiƙa mun ji labari daga iyaye da kakanni abun babu dadi. Ba ma fatan irin hakan ya sake faruwa.
2.0 Me Ke Faruwa a Yanzu?
2.1 Wacce Ƙasa ce Russia?
Russia wata ƙasa ce mai ƙarfin iko a duniya da wani mutum mai suna Vladimir Putin yake mulka a wannan zamanin, karni na 21. Tana da ƙarfin makamai sosai, tattalin arziƙi haɗi da bunƙasa. Wasu abubuwa da za ka iya sani game da ita:
– Ba ta shiri da America da NATO
– Tana ƙawance da China
– Tana da kayan yaƙi ƙwarai da gaske
– Ta ninka Ukraine sau sama da 10 a kayan yaƙi
– Tana da yawan mutanen da suka kai Miliyan 144
Taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran ƙasashe
2.2 Ina ne Ukraine?
Ukraine wata ƙasa ce da ke gabashin Turai kuma tana makwabtaka da Russia. Da suna zaune cikin lumana kafin ƙudirin sabon shugaban ƙasarsu ya tayar da hatsaniya. Matashin shugaban mai suna Volodymyr Zelensky ya nuna aniyarshi ta shiga ƙungiyar haɗakayyar ƙasashe mai suna NATO. Maƙwabciyarta Russia ta ce a’a. Ga wasu abubuwa da za ka iya sani game da Ukraine:
– Suna da yawan mutanen da ya kai Miliyan 44
– Ukraine tana maƙwabtaka da Russia
– Tana yunƙurin shiga NATO
– Tana tunanin America da NATO sune ƙawayenta
2.3 Mene ne NATO, G7, UN, EU?
– NATO (North Atlantic Treaty Organization) gamayyar ƙasashe ce da aka samar bayan Yaƙin Duniya II. Akwai ƙasashe 30 a wannan gamayyar, inda suke yunƙurin bayar da kariyar tsaro ga duk wata memba ɗinsu da aka taba. Cikin waɗannan ƙasashe akwai US, UK, Canada, France, Germany, Italy, Portugal, Turkey da sauransu.
– G7 (Group of Seven) wannan ma zauren wasu ƙasashe ne guda 7 da suka haɗa kai don samun wani tagomashi da tallafin juna a ɓangaren siyasa da tattalin arziƙi. Waɗannan ƙasashen sune: US, UK, Italy, Germany, Japan, Canada da France.
– UN (United Nations) majalisar ɗinkin duniya da aka samar bayan Yaƙin Duniya II, inda ta haɗa ƙasashe 193 a cikin 195 da suke duniya.
– EU (European Union) haɗakayyar ƙasashen Turai da ta ƙunshi ƙasashe 27.
– CSTO (Collective Security Treaty Organization) haɗakayyar wasu ƙasashen Soviet Union da suka haɗa da Russia, Uzbekistan, Kazakhstan, Tajikistan, Azerbaijan, Armenia da Georgia da sauransu.
2.4 Mece ce Alaƙar America a Cikinsu?
– America ba ta shiri da Russia
– Russia ba ta shiri da NATO da G7
– Russia tana ƙawance da China da CSTO
– China ba ta NATO da G7; a zahiri ba ta ƙawance da US, NATO ko G7Taƙaitaccen bayani game da Yaƙin Duniya –Rikicin Russia da Ukraine da mu’amalarsu da sauran ƙasashe
3.0 Mene ne Silar Faɗan Ukraine da Russia?
Ukraine ta nuna ƙudirinta na son shiga NATO amma sai Russia take son katse mata hanzari. Shugaban Russia Putin ya ce ba zai yiwu ba, don ba zai yarda a masa zagon ƙasa ba. Dalilinsa a nan shi ne, idan ya bari Ukraine ta shiga NATO, kenan an kawo masa maƙiyi har gida tunda ba ya shiri da NATO. Zai fi kyau maƙiyinka ya kasance nesa da kai, don suna maƙwabtaka da Ukraine, kenan duk abun da NATO ta ga dama za ta iya yi a Ukraine din don yi wa Russia zagon ƙasa. Putin ya ce ya gano wannan logar, don haka sai ya ƙudiri aniyar shafe Ukraine a doron ƙasa kafin ta yunƙura.
Ukraine ba ta kai Russia ƙarfin soji ba, ko kusa. Ita kawai ta dogara da NATO da kuma America. Amma NATO ta yi shiru, US kuma tana kallon abun da ke faruwa tana alhini.
4.0 Wane Sakamako Duniya Take Jira?
Duniya tana tunanin Yaƙin Duniya III zai iya kaurewa, saboda da zaran NATO da US sun yunƙuro wajen mayar martini ga Russia kan cin zalin da take yi, to haƙiƙa ita ma China da ta kasance ƙawar Russia za ta ƙaddamar da yaƙi a kan NATO da ƙawayenta. Su ma ƙananan ƙwari da ke CSTO za su kai wa Russia agaji a matsayin kara. Wannan kuma shi ake tsoro, domin shi ne zai kasance Yaƙin Duniya III a wannan ƙarnin idan ba a yi sulhu ba.
Ba ma fata ko kaɗan, amma idan hakan ta tabbata, to:
– Nahiyar Europe za ta hargitse
– Nahiyar Asia za ta hargitse
– Tattalin arziƙin duniya zai durkushe
– Africa za ta shiga halin ƙaƙa-ni-ƙaƙa
5.0 Rufewa: Yaƙi Ɗan Zamba Ne!
Yaƙi Ɗan Zamba ne! America ba za ta shiga kowane faɗa ba matuƙar ba ta yi abun da ake ƙira “analysis” ba. Sai ta caje komai ta tabbatar tana da “interest” kafin ta faɗa.
Zan maimaita, babban fatanmu a nan shi ne sulhu.
Allah Ya tsare mu, amin.
–Mohiddeen Ahmad
24th February, 2022

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA