Sabuwar dokar zabe | Buhari Ya Sanya Hannu AKan Sabuwar Dokar Zaɓe A Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan sabuwar dokar zabe wadda aka yima garanbawul domin shigo da wasu sababbin gyare-gyare a harkar zabe a Najeriya.
Shugaba Buhari ya saka hannu kan dokar ne a yayi wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon Shugaban majalisar dattawa Sen. Ahmad Lawal da Shugaban majalisar wakilai da Femi Gbajabeimila.
A cikin gyara-gyaren da aka yi ma dokar zaben kowane ma’aikacin gwamnati ko mai rike da mukamin siyasa zai aje mukaminsa a watan shidda idan har zai yi takara.
A jawabin shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramtawa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.
Daga Comr Nura Siniya.