Kannywood

Nazir ka tona asirin abinda yake boye a Kannywood inka isa ta fito kace baka taba lalata da wata a kannywood ba – Fati slow

Jarumar Kannywood Fati Slow
Jarumar Kannywood Fati Slow – Hoto: Instagram – @fatee_slow

A daidai lokacin da wasu jaruman ke kokarin sanyawa lamarin wutar da ta tashi a masana’antar Kannywood ruwa, wasu kuwa kokari suke yi su kara tada wutar ta cinye kowa ma a huta.
Ita ma a na ta bangaren jaruma Fati Slow ta fito ta tofa nata albarkacin bakin, sai dai kuma ita a nata batun tana kokawa ne kan yadda Sarkin Waka ya fito da abin da yake a rufe, kana ta nemi shima ya rantse bai taba neman wata ba kamar yadda labarunhausa na tattara bayyanai.
Haka kuma ta bayyana cewa ita babu wani darakta ko furodusa da ya taba neman ya kwanta da ita a kafin ya sanya ta a cikin fim.
Ta ce:

“Gaskiya ba zan boye maka ba, abinda kayi gaskiya kayi shirme, kuma baka kyauta ba abinda kayi, duk wadanda kuke goyon bayansa a hankali zaku gane abinda muke nufi.

“Kun zo kun tonawa mutane asiri a shafukan sada zumunta, kun zo duk abinda ake yi a Kannywood muna rufawa kan mu asiri kun bayyanawa duniya.

“Allah kadai ya san irin bakaken maganganun da aka dinga gaya mini a shafukan sada zumunta, ashe haka kuke dama, ashe baku da sirri, sai kun nemi mace kuke saka ta a fim?

“Wallahi al’umma ya fadi son ransa ne, tunda nake a Kannywood, ba a taba yi mini sallamar wulakanci ba, kuma wadannan matan da kake fada, idan zaka rantse da Allah wacece baka taba nema a ciki ba, ko kuma kace baka taba neman wata a Kannywood ba.

“Ka na da ilimin addini dana boko, yaya za ayi ka fito kana irin wadannan maganganun? Wallahi kallon babban mutum nake yi maka, bai kamata ka fito kayi wadannan maganganun ba.

“Kana tunanin cewa mutane za su soka saboda wannan maganar da kayi? ai kudin goro za ayi mana baki daya. Ya kamata ka fito kafar sadarwa kayi magana, bai kamata abinda kayi ba, kana da ilimi daidai gwargwado.

 
 
 

@fateeslow1122gmail.com #saudiya #hauntedti #yosoycreador #tiktok #usa #hasusafulaini #saudi_tiktok #saudi_tiktok #saudi_tiktok #saudi_tiktok #hauntedtiktok #saudi_tiktok #da ♬ original sound – fati slow

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button