Na kusa na yi wuff da ke da yarda Allah– Lilin Baba ga Ummi Rahab
Soyayya dai na kara karfi a tsakanin jaruman Kannywood masu tasowa wato Shu’aibu Ahmed Abbas wanda aka fi sani da Lilin Baba da Ummi Rahab kamar yarda legit na tattaro bayyanai.
Ga dukkan alamu dai soyayyar tasu za ta kai su ga shiga daga ciki nan ba da dadewa ba. Hasashen hakan ya biyo bayan wata wallafa da jarumin mawakin ya yi a shafinsa na soshiyal midiya.
Lilin Baba dai ya je shafinsa na Instagram domin taya masoyiyar tasa murnar zagayowar ranar haihuwarta a yau Laraba, 2 ga watan Fabrairu, inda ya jero zantuka masu ratsa zuciyar masoya.
Ya rubuta a shafin nasa:
View this post on Instagram
Ya rubuta a shafin nasa:
“Barka da zagayowar ranar haihuwa abar kaunar rayuwata @ummirahabofficial. Hakika ke ta daban ce mai zuciyar zinari. “Ina aika sakon zagayowar ranar haihuwa ta musamman gare ki yayin da kika kara shekara daya a yau! Ina fatan kin cika da farin ciki da annashuwa a yau. Abun farin ciki ne ganin irin matar da kika zama a yau. #HappyBirthday UMMI. “Ina miki fatan alkhairi a duniya da lahira, Allah ya ci gaba da sanya albarka a rayuwarki. Karin nasara a gare ki . NA KUSA NA YI WUFF DA KE IN SHAA ALLAH.”