Labarai

Matashi Ya Kashe Kawunsa Bayan Ya Sadu Da Matarsa

Wani Matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Tambaya Usman, ya shiga hannun ƴan sanda, bayan ya kashe kawun sa, Umar Musa, saboda ya kama shi, yana saduwa da Matar sa a Jahar Niger.Matashi Ya Kashe Kawunsa Bayan Ya Sadu Da Matarsa
Lamarin ya faru ne a farkon watan nan a Kauyen Jaguwa ta Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jahar.
Gidan jaridar Jakadiya Rvt ce ta ttataro yadda al’ammarin ya wakalana Usman wanda ya tabbatar da aikata ta’addancin, yace ya sassari Mutumen a kanshi, saboda ya kasance yana kwanciya da matar shi a lokutan da suka gabata.
“Na kama Umar yana saduwa da Mata ta a gadona, a dalilin haka, Ni kuma nayi amfani da adda na sassare shi,kuma ya mutu.
“Na kama shi da irin wannan laifin da yawa, amma iyayena da ƴan uwana suka shiga lamarin, ta hanyar gargaɗin sa domin ya bari.
“Ya bani haƙuri, kuma yayi alƙawarin bazai kara ba, amma abun mamaki na sake kama shi, amma na tura shi lahira,da adda ta ta hanyar saran shi a saman kai.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Wasiu Abiodun ya Tabbatar da labarin, yace an tura shi Kotu da tuhumar kisan kai

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button