Maganar sarkin waka Nazir Gaskiya ce, amma idan ya cika ya fit ya ranste vai tana neman wata da lalata a kannywood ba – Ty shaba
Da anyi hakurin da bata kai ga zakulowar wasu maganganu da suka dinga biyo baya ba, wanda wasu akan yi sune dan mayar da martani da bata wanda ya fara taba su, wasu kuma na iya zama gaskiya shima da nashi kashin a gindi, tsautsayi ya kai shi tabo su.
‘Yan Kannywood sun yi caa akan Sarkin Waka
A cikin makon nan dai kun ji yadda ‘yan masana’antar Kannywood suka dinga yiwa Sarkin Waka saukale shi da dan uwanshi kan batun rike hakkin jama’a, amma sai dai wannan bashi ka dai bane batun da ya bata ran ‘yan masana’antar ba har da batun cewa ana lalata da mata kafin a saka su a fim.
Jaridar internet Labarunhausa ta ruwaito cewa hakan ya fusata ‘yan masana’antar matuka, domin magana ce da aka dade ana zargin masana’antar da ita, sai gashi dan cikinta, wanda za a iya kiran shi da dan gado, domin ‘yan uwansa biyu ne masu shirya fim da bada umarni a masana’antar, hakan na nuni da cewa ya san komai a masana’antar tun kafin ya shiga.

Nazir ya fito yayi zargi a bainar jama’a, wanda hakan shi ya tabbatar da wancan tsohon zargin, wanda sun sha musantawa, sai dai ko masu musantawar sukan musanta ne akan kansu.
A shekarun baya an taba yin irin wannan tonon sililin a Kannywood
Idan muka koma baya wata shekara da wani bala’i ya fadawa masana’antar ta Kannywood, inda har gwamnatin jihar Kano ta dakatar da sana’ar, a lokacin saboda karfin da Kano take dashi akan harkar saboda yawan ‘yan Kano da suke masana’antar da kuma kasuwar fim dake Kano ya sanya harkar ta durkushe a wancan lokacin.
Jarumai mata a wancan lokacin duk da babu kafafen sada zumunta, sun dinga shiga gidajen radio suna tona asirin masana’antar, inda dattijai dai-dai ne suka tsame daga cikin su, irin su Usaini Sule Koki, da sauransu, suke cewa su kadai suke gani da mutunci.
Haka suka dinga yiwa sauran kudin goro, saboda an bayyana sunayen su a cikin wadanda za a kora daga masana’antar domin tsaftace ta, to sai kuma gashi kwatsam, an sake kwatawa a wannan shekarar, wannan dai kamar dabi’a ce ta ‘yan fim, idan suna cikin fushi su dinga tonawa kan su asiri.
TY Shaba ya yiwa Sarkin Waka wata tambaya
Wannan tonon silili da Sarki yayi yasa wasu mata daga masana’antar sun fito sun karyata batun da kuma ware kansu koda ana yi banda su, sai dai TY Shaba ya jefawa Sarkin Waka tambayar, idan zai iya rantsewa shi bai taba amfani da wata ba a masana’antar?
TY Shaba duk da ya bata fuskar sa ya wallafa bidiyon a shafinsa, inda a cikin bidiyon ya nemi Sarkin Waka yayi rantsuwa bai taba neman wata kafin ya sata a waka ko fim ba, inda a kasa ya rubuta Kannywood dai ta mu ce, kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani.
View this post on Instagram
Uhm Allah dai yakyauta yakuma gyaramana gabaki daya