Labarai

Lokacin juyin mulki ya wuce a Nijeriya – in ji Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a sake yin juyin mulki na sojoji a Nijeriya ba.

Buhari ya faɗi hakan ne a wani martani kan damuwar da gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya nuna kan guguwar juyin mulki da ta taso a Afirka da ta haɗa da hamɓare gwamnatocin domokraɗiyya a Mali, Guinea da Burkina Faso.

Kamfamin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Buhari ya ce ya na da ƙarfin yaƙinin cewa Nijeriya ta wuce lokacin yin juyin mulki.

Buhari ya baiyana haka ne a wata liyafa da kwamitin ƴan siyasa, ƴan kasuwa, ƴan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ka haɗa a fadar shugaba kasa a jiya Litinin.

A watan Nuwambar 2021 ne Buhari, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, ya jaddada cewa Afirka ba za ta lamunci juyin mulki ba bayan da a ka yi juyin mulki a Guinea da Mali.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button